Ilimi
Babu Malamin Da Aka Biya Albashi Tun Watan Fabrairu — Inji Emmanuel Osodeke
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) a ranar Talata ta ce babu daya daga cikin malaman jami’o’inta da aka biya albashi tun bayan da kungiyar ta fara aiki a watan Fabrairu.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin Sunrise Daily, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya zargi Gwamnatin Tarayya da amfani da yunwa a matsayin makami wajen tilastawa malaman da ke yajin aikin komawa ajujuwa.
Osodeke ya bayyana cewa an kwashe watanni 6 ba a biyansu albashin, ya ce gwamnati mai ci ba za ta iya amfani da karfin yunwa wajen ja da ‘yan kungiyar da ke yajin aiki ba.
A cewarsa, gwamnatin tarayya na ganin cewa hana malaman jami’o’in albashi zai sa malaman jami’o’in durkushewa tare da kawo karshen yajin aikin.
“An janye albashin mu, wata na shida kenan ko albashi ba a biya ba. Sun yi tunanin idan sun rike albashin mu na wata biyu ko uku za mu zo bara mu ce ‘a taimaka ku bar mu mu koma bakin aiki,” in ji Shugaban ASUU.
“Amma mu a matsayinmu na ƙungiyar masu hankali, mun girma fiye da haka. Ba za ku iya amfani da karfin yunwa don ja da ‘ya’yanmu ba wanda shi ne ainihin abin da gwamnati ke yi.”
ASUU na zargin gwamnati da kin sauraron bukatunsu.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin domin matsawa bukatunta na samar da ingantaccen tsarin walwala da inganta fannin ilimi da dai sauran su, lamarin da ya tilastawa daliban Najeriya zama a gida.
Da yake nuna damuwa kan rikicin Jami’o’i da ya kunno kai, a ranar 19 ga watan Yuli shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministan ilimi Adamu Adamu da ya ba da mafita kan wannan kalubalen tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu.
A yau ne wa’adin shugaban kasa zai cika kuma ASUU ta tsaya tsayin daka har sai an biya bukatun ta. Wannan ci gaban bai dame su ba, kungiyar ta kara tsawaita yajin aikin da wasu makonni hudu, wanda hakan ya kawo cikas ga fatan daliban na komawa makaranta.
Da yake mayar da martani ga umarnin Buhari na kawo karshen yajin aikin, Farfesa Osodeke ya dage cewa har yanzu kungiyar a bude take don tattaunawa da wakilan gwamnati domin kawo karshen takaddamar masana’antu.
Ya ce babu inda za a yi dangantaka ta ubangida da bawa a duniyar ilimi, yana mai cewa ma’aikata na da ‘yancin sukar manufar da ba ta dace ba.
Shugaban ASUU ya yi tir da tsarin Integrated Payroll and Personnel Information System (IPPIS), wato tsarin hade bayanan kudin ma’aikatu, tsarin da gwamnati ba za ta yi amfani da shi wajen biyan malaman albashin su ba.
