Connect with us

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: Ƴan bindiga sun sake sako mutane 5 cikin fasinjojin jirgin Abuja zuwa Kaduna da suke tsare da su

Ƙarin wasu mutane biyar da ƴan bindigar da suka sace su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris sun shaƙi iskar ƴanci.

Rahotonni sun bayyana cewa mutanen biyar dukkan su maza sun kuɓuta ne a yau Talata.

Kafar Talabijin ta Channels, ta bayyana cewa har zuwa lokacin da ta fitar da labarin mahukuntan Najeriya ba su magantu ba dangane da sakin mutanen.

Sai dai tashar ta ce, mamba a tawagar da ke sasanci wajen ganin an sako mutanen Tukur Mamu ya tabbatar da sakin nasu a yau 2 ga watan Agusta.

Haka kuma, Mamu, ya bayyana sunayen mutanen biyar da aka sako da suka haɗa da: Farfesa Mustapha Umar Imam wanda ke aikin jinya a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato da Akibu Lawal da Abubakar Ahmed Rufai da Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.

Haka kuma Channels ta ruwaito cewa ba a bayyana ko an biya ƴan ta’addar kuɗin fansa ba gabanin sako mutanen biyar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet