Connect with us

Kasuwanci

Jami’an hukumar EFCC sun kai samame kasuwar canjin kuɗi ta Wapa

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, sun yi wa kasuwar canjin kuɗin ƙasashen ƙetare ta Wapa dirar mikiya.

Jaridar Solacebase ta tawaito cewa jami’an hukumar sun yi wa kasuwar zuwan bazata ne wadda ke unguwar Fagge da safiyar yau Alhamis.

Haka kuma ta ruwaito cewa bayan dirar ma’aikatan na EFCC ne ƴan kasuwar da dama suka riƙa neman mafaka yayin da wasu suka rufe shagunansu don gudun kamun jami’an.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an na EFCC na gudanar da bincike ne kan zargin da ake yi na cewa wasu mutane suna yin sama-da-faɗi kan kuɗaɗe tare da ɓoye kuɗaɗen ƙasashen waje wanda hakan ke haifar da karanci da kuma ta’azzara tsadar canjin su musamman ma Dalar Amurka.

Solacebase ta kuma bayyana cewa ƴan kasuwar sun sha mamakin yadda jami’an da suka je kasuwar cikin motocin bas guda uku tare da shaida musu cewa kada su firgita domin ba kame za su yi ba kawai za su wayar da kan su kan rage taɓarɓarewar canjin Dala da ake yi zuwa Naira.

Haka kuma jaridar ta ce, ta yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumar ta EFCC shiyyar Kano sai dai ba ta ce komai ba kan zuwan su kasuwar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet