Connect with us

Labarai

Ƴan bindiga sun sake sako mutane 7 cikin fasinjojin jirgin Abuja zuwa Kaduna

Bayan shafe tsawon kwanaki 135 da kai hari kan jirgin ƙasa tare da sace fasinjoji, ƴan bindiga sun sake sakin mutane bakwai cikin fasinjojin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.

Rahotonni sun bayyana cewa, Ƴan bindigar sun sako mutanen ne a yau Laraba.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Wani mamba a kwamitin da ke shiga tsakanin ƴan ta’addan da iyalan mutanen da ke hannunsu Tukur Mamu a wata sanarwa da ya fitar, ta ce shida daga cikin wadanda aka sako ƴan gida ɗaya ne watau ma’aurata da ƴaƴansu huɗu.

Haka kuma, Sanarwar ta ce an sako mutanen ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani.

Mahaifin yaran Abubakar, ɗa ga tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Kano da Benue, Manjo Janar Idris Garba Mai ritaya ne.

Haka kuma sun sako wata mata mai shekaru 60 Hajiya Aisha Hassan wadda aka ce an kubutar da ita ne sakamakon kalubalen rashin lafiya da ke damuna.

Ɗangin su shida da ƴan ta’addan suka sako sun haɗa da Abubakar Idris Garba, mahaifin ƴaƴan nasa hudu sai matarsa ​​Maryama Abubakar Bobbo da babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10.

Sauran sun haɗa da Fatima Abubakar Garba ƴar shekaru bakwai da Imran Abubakar Garba mai shekaru 5 da ƙaramar Zainab Abubakar Garba mai shekara ɗaya da rabi.

Sai dai ba a bayyana ko an biya kuɗin fansa ga ƴan bindigar ba gaban in sakin nasu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet