Labarai
Idan na zama shugaban ƙasa ASUU ba za ta sake yin yajin aiki ba- Atiku
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce matuƙar ya zama shugaban Najeriya, to ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ba za ta sake shiga yajin aiki ba.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a wajen bikin ranar matasa ta duniya da aka gudanar a Abuja yau Juma’a.
Atiku Abubakar, ya ce, mahaifinsa bai so ya je makarantar boko ba, amma daga baya ya jajirce da kuma shiga makaranta har zuwa matakin jami’a.
Haka kuma ya ƙara da cewa haƙƙin kowane matashi shi ne samun ilimi, tare da nanata cewa yajin aiki da ƙungiyar ASUU ke yi da kuma rashin magance matsalar su da gwamnati ta gaza yi abun damuwa ne.
Ya kara da cewa hakan ba za ta taba faruwa ba a karkashin gwamnatin PDP ko kuma gwamnatinsa idan aka zabe shi.
Haka kuma, ya ce shi mutum ne mai bunkasa harkokin ilimi, inda ya kuma ce hakkin kowace gwamnati ne ta tabbatar an bai wa kowani matashi a kasar hakkokinsa musamman a bangaren ilimi.
