Connect with us

Labarai

Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 50 tare da rushewa gidaje da dama a Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar mutane hamsin tare da raba wasu da gidajen su sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassa na jihar.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Alhaji Yusuf Sani Babura, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Asabar a Dutse.

Ya ce ambaliyar ruwan ta lalata dubban gidaje a jihar, tare da dukiyoyin al’umma.

Haka kuma ya ƙara da cewa lamarin ya kuma tilastawa mazauna yankunan da Abin ya shafa fakewa a wasu wurare da suka hada da gine-ginen da gwamnati ta yi.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki mutanen da suka rasa matsugunansu idan ta Kai su sansanonin wucin gadi guda goma sha ɗaya.

Wasu daga cikin mutanen da iftila’in ya shafa mazauna garin Balangu ne inda akalla gidaje ɗari biyu da talatin da bakwai suka rushe tare da mutuwar mutane hudu.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, A ƙoƙarin gwamnatin tarayya na tabbatar da bada agaji, ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta ziyarci jihar domin raba kayan agaji.

Ta kasance a jihar ne tare da Babban Daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Mustapha Habib, domin bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Ministar ta ce zuwanta jihar ya samo asali ne daga umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na bayar da tallafin da ya kamata ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa abin da ya bayyana da daukar matakin gaggawa kan lamarin.

Sai dai Gwamna Badaru, ya koka bisa yadda ambaliyar ta afku, inda ya ce lamarin ya haifar da rudani ga wadanda abin ya shafa.

Gwamnan ya yi fatan cewa tallafin da gwamnati za ta yi zai ragewa jama’ar radadi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet