Labarai
Ana Zargin Da Hadin Bakin Wasu Jami’ai Ake Sace Kudaden Kananan Hukumomi
Sakataren kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa (ALGON) kuma shugaban karamar hukumar Lapai, Mu’azu Jantabo ne, ya yi wannan zargi cewa wasu daga cikin hukumomin jihar na hada baki da jami’an kananan hukumomi wajen sace kudade a jihar.
Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a wani taron da aka gudanar don magance rikicin da ya kunno kai tsakanin shugabannin kananan hukumomi da ma’aikata kan batun biyan albashi, Jantabo ya ce akwai ma’aikatan bogi da ma’aikatan da ba su cancanta ba a dukkan kananan hukumomin 25 da suka hada da wadanda ba su kammala karatun sakandare ba.
Da yake bayar da misali da karamar hukumarsa, shugaban ya ce, “A yanzu haka lissafin albashin mu a karamar hukumar Lapai Naira miliyan 130 ne a kan albashi kadai kuma muna da wasu alkawurra kamar gudummuwar jami’ar IBB da aka fi sani da cirewa doka, hukumar yi wa kananan hukumomi hidima da sauransu.”
“Idan muka hada dukkan nauyin da ke wuyan mu, ya kai sama da Naira miliyan 200. Kuma kamar yadda aka ce tun lokacin da na hau mulki, mafi girman kason da muka samu a karamar hukumar dina shi ne Naira miliyan 175. Don haka, idan ka duba, a kowane wata, muna da gibin kusan Naira miliyan 50.”
Ya kuma ce jerin sunayen ‘yan fansho na kananan hukumomin cike suke da sunaye kagaggu, sunaye na gaskiya sune 189 kacal cikin sunaye 445 da hukumar fansho ta kawo.
“Mun gano cewa sama da sunaye 40 na cikin wadanda suka mutu. To, wanene yake karbar wadannan fensho? Bayan haka, asusun fanshonmu ya ragu da kusan Naira miliyan 10,” inji shi.
Ya ce ya tura fasahar da zarar ma’aikaci ya yi ritaya, za a cire sunansa kai tsaye daga jerin sunayen ma’aikata, inda ya ce hatta wasu ma’aikatan kudi na kananan hukumomi suna sha’awar rashin biyan wasu ma’aikata albashi da kuma karbar wasu kudade da kansu.
Jantabo ya yi kira ga gwamnatin jihohi su baiwa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu ta yadda suma za su iya cin gashin kansu na siyasa da mulki.
“Ba zan iya samun iko kan albashi ba; muna karamar hukuma kuma wani wanda albashinsa ya kai Naira 40,000 yana hada baki da akawu a Minna kuma suna biyansa Naira 150,000 duk wata. ”
“Don haka, sai dai idan ba za mu iya magance duk wadannan matsalolin ba, to a lokacin ne muka dace mu yi aikin cin gashin kai,” in ji shi.
