Connect with us

Featured

Asibitin Best Choice Specialist Ya Mallaki Na’urar Endoscopy Irinta Ta Farko A Kano

Shugaban Best Choice Specialist Hospital da ke Kano unguwar Sabuwar Gandu Auwal Muhammad Lawal, ya bayyana cewa a halin yanzu asibitin ya samu sabuwar na’urar da za a dinga amfani da ita don samun nasara da kuma sauƙaƙa ayyukansu, kuma ita ce irinta ta farko a fadin jihar Kano.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata a birin Kano.

Malam Auwal yace, ita wannan na’ura za ta sauƙaƙa aikin tiyata musamman ga cututtukan da suka shafi Mafitsara da Ƙoda da kuma fitar da ƙarin mahaifa.

Hakazalika na’urar za ta iya gano matsalar ciwon ciki da ciwon daji wanda wannan wani kari ne a cikin jerin kayan aikin fasaha dake asibitin.

A cewar Auwal Lawal, suna da wadatattun ma’aikata da ƙwararrun Likitoci don biyan buƙatun al’umma.

A halin yanzu Asibitin Best Choice yana da likitoci na dindindin guda Ashirin (20).

Sannan ga kuma ƙwararrun likitocin a kowane fanni.

Auwal ya ƙara da cewa, Asibitin ya fara ne da ɗakunan da basu wuce huɗu ba, amma a yanzu yana iya alfahari da cewa sun samu ƙarin ɗakunan kwanciya da gadaje sama da arba’in.

Shugaban ya ci gaba da cewa “Babban burin da muka saka a gaba a wannan asibitin shi ne, taiimakawa al-umma duba da irin wahalar da mutane suke sha a fannin lafiya.”

“Asalin Asibitin namu clinic ne, daga bisani muka faɗaɗa tunaninmu ya koma specialist, wato muna iya tunkarar kowace irin cuta kenan da yardar Allah kuma a samu nasara”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet