Labarai
Shugaba Buhari ya sake naɗa Bashir Ahmad a matsayin babban mai taimaka masa kan sadarwar zamani
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya naɗa tsohon mai taimaka masa akan harkokin kafafen sada zumunta Bashir Ahmad, a matsayin babban mai taimaka masa na musamman kan sadarwar zamani.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ne ya tabbatar da sabon naɗin nasa a wata takardar ɗaukar aiki da ya aike wa Bashir Ahmad, ɗin.
Haka kuma ta ƙara da cewa, takardar wadda aka gano ta jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja, a cikinta Boss Mustapha ya ce, naɗin Bashir Ahmad a wannan sabon muƙami ya fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Yulu, 2022.
