Labarai
Hukumar KAROTA ta cafke ƴan Adaidaita Sahu 3 bisa jargin su da sace wayoyin fasinja
Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa KAROTA ta cafke wasu mutane su uku da zargin sace wayar Fasinja a cikin Baburin Adaidaita Sahu.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jam’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar da yammacin yau Laraba.
Sanarwar ta ce, waɗanda ake zargin sun haɗa da; Aminu Musa Ibrahim Rigasa ɗan asalin jihar Kaduna da Aminu Isah Usman Rimin Keɓe ɗan jihar Kano da kuma Usman Sani Gwaram ɗan jihar Jigawa.
Haka kuma, KAROTA ta ce, bayan da ta samu nasarar cafke matasan, sun bayyana mata cewa sun shafe fiye da shekara guda suna aikata wannan mummunar ta’adar ta ɗaukar fasinja a cikin babur ɗin Adaidaita Sahu mai Lambar KYW 291 AY wanda yake ɗauke da Koriyar lamba guda biyu TRN-5767 da KRY- 0913.
Mutumin da ake zarginsu da sace wa wayar mai suna Malam Shitu Umar Birnin Kudu ya bayyana cewa bayan ya tsayar da Adadinta Sahu ya tarar da mutum biyu a ciki suna cikin tafiya sai ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya kara masa wata babbar Jaka da take hannunsa a lokacin sai suka ɗauke masa waya, bayan sun ɗauke sai suka ce masa ba inda ya bayyana musu tunda fari su je ba.
Haka kuma ya ƙara da cewa bayan da ya sauka ne sai ya fahimci sun ɗauke masa waya, bayan ya ari wata wayar ya kira sai aka ce masa ga wayarsa a hukumar KAROTA an kama waɗanda suka ɗauka.
Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya bayyana wa humar KAROTA inda suke kai wayar idan sun sata da kuma sunan wanda suke sayar wa.
Hukumar ta sami nasarar cafke matasan ne bayan sun ɗauke wayar Shitu Umar sun gudu da ita.
Dubunsu ta cika ne lokacin da suke ƙoƙarin ɗaukar wayar wani magidanci bayan da suka ɗauke shi sai ya fahimci ɓarayin waya ne a inda ya nemi taimakon jami’an KAROTA waɗanda suke tsaka da gudanar da aiki a shatale-talen gadar Ƙofar Nassarawa ƙarƙashin jagorancin Halilu Kawo Jalo.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, hukumar ta miƙa waɗanda ake zargin ga rundunar ƴan sandan jihar Kano domin faɗaɗa bincike tare da cafke wanda suka ce suna sayar wa da wayoyin.
Shugaban Hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya buƙaci al’umma da su cigaba da sa ido a duk lokacin da za su hau Baburin ɗin Adaidaita Sahu tare da lura da Koriyar lambar jiki.
