Featured
Rurum ya samu kyauta ta musamman daga wata cibiya a kasar Rwanda
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Wakilin Kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum ya samu kyautar kasancewa gwarzon dan majalisa kuma guda cikin waɗanda cibiyar kula da Majalisun Kasashe ta gayyata taronta domin karramashi.
Taron da aka gudanar a birnin Kigali, ya samu halartar wasu cikin wakilan majalisun dokokin kasahen Afrika..
Shugabar Rwanda Cooperation Amb. Christine ce ta miƙa wannan katafariyar kyauta ga Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum, wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure a majalisar wakilan tarayyar Najeriya.
