Labarai
Ganawa Da Tinubu ‘Yan Uwatakace Fiye Da Siyasa – Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Asabar ya nemi bayyana dalilin da ya sa ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu kwanan nan.
A wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Kehinde Akinyemi, tsohon shugaban kasar ya nuna rashin gamsuwa da rahotannin da ba su yadda da shi ba na abin da ya tattauna da Tinubu a asirce.
Ya ce tattaunawar a yayin ziyarar ta kasance “yan uwantaka fiye da siyasa”.
Obasanjo ya ce Tinubu ya bukaci da kada kowane bangare ya fito fili ya bayyana abin da aka tattauna a taron.
“Wadanda ke ikirarin cewa su ‘yan cikin gida ne a wurin taron suna ba da sanarwa kan tattaunawar da kuma wadanda ke yaba min maganar da ban yi ba, makiyan bakon ne kuma ba sa yin wani abin azo a gani na ziyarar,” in ji Obasanjo.
