Labarai
Hukumar NBC Ta Tsawaita Wa’adin Dakatar Da Tashoshin Yada Labarai
Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa ta jinkirta rufe gidajen rediyon da talabijin da ta ce ba su sabunta lasisin su ba.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Hukumar ta yi barazanar soke lasisin watsa shirye-shiryen talabijin na Silverbird TV, AIT, Raypower FM, Rhythm FM da sauran tashoshi saboda gaza sabunta lasisin su.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Bashin da ake bin gidajen , NBC ta ce, ya kai Naira biliyan 2.66.
Ta kuma shawarci tashoshin da su rufe ayyukansu cikin sa’o’i 24.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar din nan, hukumar ta NBC ta ce ta kara wa’adin rufewar har zuwa ranar Laraba.
“Wannan shi ne sanarwa ga da duk gidajen talabijin da rediyon da abin ya shafa, da aka soke lasisin su tare da ba su sa’o’i 24 su biya duk wasu kudaden lasisin da Hukumar kula da kafafen yada Labarai ta Kasa ta tsawaita wa’adin wanda za a biya dukkan basukan daga sa’o’i 24 zuwa Laraba 23 ga Agusta, 2022. ” wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan hukumar NBC, Balarabe Shehu Ilelah, ta ce.
“Duk gidajen watsa labaran da abin ya shafa wadanda suka kasa biyan basussukan su biya a ko kafin ranar 23 ga Agusta, 2022 an umurce su da su rufe da karfe 12 na daren ranar 24 ga Agusta, 2022, gidan talabijin na channels ne ya rawaito hakan.
“Wannan tsawaitawa ta faru ne saboda roko da Tashoshin Watsa Labarai da abin ya shafa, masu ruwa da tsaki, mutane da kungiyoyi masu kishin jama’a suka yi.”
