Ilimi
Jami’ar Cyprus Ta Kori Daliban Najeriya Daga Jihar Zamfara
Akalla dalibai 91 ne jami’ar Cyprus International University ta kora daga jihar Zamfara saboda gazawar gwamnatin jihar Arewa maso Yamma wajen biyan kudin makaranta da sauran kudade.
Daliban da ke samun tallafin karatu a jami’ar, an kori daliban ne saboda Zamfara ba ta cika yarjejeniyar bayar da tallafin karatun shekarun da suka gabata ba.
Nigeria Abroad ta ruwaito cewa wasu daga cikin daliban da suka zanta da Sashen Hausa na BBC a ranar Litinin din da ta gabata, sun yi kukan cewa suna fuskantar yunwa, da kuma barazana, baya ga cewar takardar izinin zama na su ya kare kuma hukumomi na iya kama su saboda kasancewa su a cikin kasar ba bisa ka’ida ba.
Daya daga cikin daliban da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Mun fara samun matsala tsakanin makarantar da gwamnatin jihar Zamfara tun shekara ta farko da muka yi makaranta amma muna tunanin za a iya magance ta ba tare da daga murya ba.
“Lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ta aiko mu nan (Cyprus), sun kulla yarjejeniya da makarantar. Amma daga dukkan alamu, wadancan ko bangare na yarjejeniyoyin ba a cika su ba, don haka rashin dacewar makarantar.
“Alal misali, lokacin da muke zuwa nan (Cyprus), sun gaya mana cewa an biya kuɗin makarantarmu na ’yan shekaru. An kuma gaya mana cewa za a biya mu alawus na dala 100. Amma da muka zo da farko sun ba mu wasu kudade amma ba su kai dala 100 ba kamar yadda suka yi alkawari, kuma shi ne matsala ta farko.
“Wannan ita ce shekarar mu ta uku a kasar nan kuma lamarin ya yi kamari. Ya kai ga makarantar ta ce ba za su kara yarda da mu ba, kuma sai da suka kore mu daga makarantar, su ma sun kore mu daga dakin kwanan dalibai wato hostel. A halin yanzu, ba mu da matsuguni, abun baƙin ciki kuma ba mu san abin da za mu yi ba.
“Ba mu da abinci kuma ba mu da matsuguni masu dacewa saboda makarantar ta kore mu daga dakunan kwanan dalibai. Da yawa daga cikinmu sun koma barci a Masallatai da sauran wuraren da wasu marasa lafiya ne. Ba mu san inda wasu daga cikin daliban suke yanzu ba, amma na yi imanin cewa da yawa daga cikinsu sun sami hanyar tsira. Wannan shi ne wata na biyu da muke cikin wannan hali na rashin mutuntaka a nan.”
Ya ce sun tuntubi gwamnatin jihar Zamfara ta hanyoyi da dama game da halin da suke ciki domin su samu bakin zaren warware wannan matsala, amma ko dai sun gaza yin aiki da sauri.
Ita ma wata daliba da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa suna cikin mawuyacin hali wanda ke bukatar kulawar gwamnatin jihar Zamfara cikin gaggawa.
Ta ce: “Mu dalibai mata 10 ne da ke zama a wani lungu a inda muka tsinci kanmu. Mafi munin lamarin dai shi ne yadda jami’an ‘yan sandan Cyprus da sauran jami’an tsaro suka yi mana barazanar kama mu, saboda shekara uku kenan ba mu biya kudin izinin zama ba. Don haka, muna fuskantar babbar barazana. Ba ma fita yanzu don gudun kada ‘yan sanda su kama mu wanda hakan na iya haifar da daurin da zai dau shekaru.”
A cewar rahoton, gwamnatin jihar Zamfara da aka tuntube ta kan lamarin ta tabbatar da halin da daliban ke ciki a kasar Cyprus, kuma ta fara aikin yadda za ta magance matsalolin.
Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya tabbatarwa da sashen Hausa na BBC cewa an biya wani bangare na kudaden da ake bin jami’ar da kuma batun kwanan daliban.
Dosara ya ce, “Muna aiki don biya a cikin gaggawa. Ban da haka, gwamnatin jihar ta yi yarjejeniya da jami’ar Cyprus cewa za a biya ragowar kudin da wuri.
“Har ila yau, ya kamata waɗannan ɗaliban su sani tun daga ranar farko cewa za a iya shaida wasu ƙalubale a cikin karatun a ƙasashen waje amma hakan ba yana nufin mun yi watsi da su.” Kamar yadda jaridar Alkiblah ta rawaito.
