Labarai
Bayan Yi Masa Tiyata Osinbajo Ya Halarci Zaman Majalisar Zartaswa
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, a karon farko a yau Larabar, ya halarci taron majalisar zartarwa ta tarayya da ya saba gudanuwa a Abuja.
Wannan shine karon karon Farko da ya bayyana, tun bayan da aka yi masa aikin tiyata cikin nasara a ranar 16 ga watan Yuli, a wani asibitin dake Ikejan jihar Lagos.
An yi masa tiyatar ne bayan karaya da ya samu a kafarsa, kuma raunin da ya samu a kafar tasa ya addabar shi, lamarin daya tilasta masa zuwa don ayi masa aiki.
Osinbajo, wanda aka sallame shi a ranar 25 ga watan Yuli, yana samun murmurewa a gida kuma kusan yana halartar Wasu daga cikin ayyukan gwamnati.
Mataimakin shugaban kasar ya samu tarba daga ministoci da hadiman shugaban kasa a taron majalisar ministocin tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta. Daukacin wadanda suka saba halartar zaman suma su halartar.
