Featured
Ronaldo na da makoma mai kyau a Manchester United – Erik ten Hag
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Erik ten Hag ya ce har yanzu Cristiano Ronaldo ya na da makoma a kungiyar a karkashin jagorancinsa, duk kuwa da cewa ya ajiye shi a benchi a wasan da suka doke Liverpool a Old Trafford a ranar Litinin
Ronaldo ya dumama benci a wasan da Manchester United suka bai wa yaran Jurgen Klopp mamaki da kwallaye 2-1, kwallaye biyun da ‘yan wasa Jadon Sancho da kuma Marcus Rashford suka zura a raga.
Sancho da Rashford sun taka rawar gani a gaban Manchester United a wasan, tare da taimakon Anthony Elanga amma Ten Hag ya yi imanin cewa Ronaldo na iya haskawa a salon wasansa.
Ten Hag ya ce batun shekarun Ronaldo ba wata matsala ba ce, yana mai cewa “idan ka iya wasa, kuma kana bada abin da ake bukata kana da amfani sosai”.
Yayin wasan na ranar litinin dai Ten Hag ya hakura da amfani da Ronaldo mai shekaru 37 da kuma Harry Maguire wanda kuma salon ya taimaka wajen kai kungiyar ga nasara.
