Featured
Kano: Gini ya danne wasu ƴan kasuwar sayar da wayoyi ta Beirut
Wani bene mai hawa huɗu da ake tsaka da ginawa a Kasuwar sayar da wayoyin salula ta Beruit Road a Kano ya rubto, inda ake fargabar ya danne wasu ƴan kasuwar.
Wasu daga cikin ƴan kasuwar sun shaida wa manema labarai cewa iftila’in ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yammacin yau Talata.
Tuni dai jami’an tsaro da hukumomi daban-daban har ma da jami’an hukumar bada agajin gaggawa NEMA da sauran jami’an aikin ceto suka shiga fafutukar ceto mutanen.
