Jajen nasa dai na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar Kano Malam Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya fitar a Talatar makonnan.
Sanarwar ta ruwaito cewa, Sarkin bayyana alhininsa game da ambaliyar ruwan da aka samu a wasu sassan jihar Kano.
Haka kuma ta cikin sanarwar, mai martaba sarki ya buƙaci al’umma da su guji zubar da shara a hanyoyin ruwa domin kauce wa afkuwar ambaliya a gaba.
Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma jaddada buƙatar malamai da su ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kai domin magance matsalolin ambaliya da ke yin sanadiyyar salwantar rayuka da asarar dukiya har ma da rasa matsugunai.