Connect with us

Labarai

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Bar Najeriya Zuwa Amurka

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a safiyar ranar Larabar nan ya tafi kasar Amurka domin neman hadin kan duniya da goyon baya ga shirin da Najeriya ta kaddamar da shi a kwanan nan.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya fitar ta ce Osinbajo zai gana da takwaransa na Amurka, Kamala Harris; Kungiyar Bankin Duniya, da sauran abokan hulda.

Tafiyar na zuwa ne kimanin wata guda bayan nasarar yi wa Osinbajo tiyata.

Osinbajo ne ke jagorantar kungiyar samar da wutar lantarki ta Najeriya a kan ayyukan Amurka tare da tarukan da za a fara daga ranar 1 ga Satumba don inganta shirin da kuma samun tallafin duniya daga gwamnatin Amurka, kamfanoni masu zaman kansu, da sauran abokan ci gaba.

Shirin Canjin Makamashi na Najeriya da aka kaddamar a makon da ya gabata an ce yana bukatar akalla dala biliyan 10 a duk shekara sama da kasuwanci kamar yadda aka saba kashewa don aiwatarwa mai inganci.

A wajen kaddamar da shirin, Bankin Duniya da wata kungiyar makamashi – Sun Africa, sun yi alkawarin bayar da dala biliyan 1.5 kowannensu wanda ya kai dalar Amurka biliyan 3 na farko don tallafawa aiwatar da shirin samar wutar lantarki a Najeriya.

Mataimakin na Najeriya zai kuma gana da sakatariyar makamashin Amurka, Jennifer Granholm; Sakatariyar Baitulmali, Janet Yellen; da shugaban bankin duniya David Malpass; da sauransu.

Tawagar mataimakin shugaban kasar Amurka za ta hada da ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu; Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi; Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva; da sauransu.

Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Ana sa ran Osinbajo zai dawo Abuja a farkon mako mai zuwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet