Labarai
Umarnin Shugaban Kasa Ga Hafsoshin Tsaro Yana Samun Sakamakon Da Ake Bukata – Minista
Ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya ce umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa hafsoshin sojan kasar domin farauta, bibiya, da kuma magance ‘yan ta’adda da yaren da suke fahimta ya fara samar da sakamakon da ake bukata.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Talatar nan a Kano, yayin wani taron yini biyu na kasa kan al’adu, zaman lafiya da tsaron kasa, wanda cibiyar kula da al’adu ta kasa (NICO) ta shirya.
“Sojoji sun samu nasarori wajen kawar da ayyukan ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da sauran nau’ikan laifuka a fadin kasar,” in ji shi.
Mohammed, wanda ya samu wakilcin Darakta mai kula da harkokin al’adu na kasa da kasa, Memunat Idu-lah, ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta aike da kudirori guda biyu ga majalisar dokokin kasar kan yadda za a kula da bama-bamai, da kuma kananan makamai.
“Har ila yau, gwamnatin a yanzu tana yin hulɗa mai ma’ana tare da mambobin kungiyar ECOWAS, da sauran yankunan shiyya don magance matsalar rashin tsaro a Najeriya,” in ji shi.
Ministan ya bayyana cewa, karkatar da rahotanni, da kuma abubuwan da suka faru na labaran karya, kalaman kiyayya, da kuma rashin bayar da bayanan sun taimaka wajen tabarbarewar harkokin tsaro a Najeriya.
Daily Trust ta rawaito cewa, A nasa bangaren, babban sakataren hukumar ta NICO, Ado Muhammad Yahuza, ya bayyana cewa taron shi ne babban shirin cibiyar domin sanin alakar da ke tsakanin al’adu da ci gaban kasa.
“Don cimma hakan, kowace shekara cibiyar tana mai da hankali kan muhimman masu ruwa da tsaki da wayar da kan su. Wannan don a yaba da irin rawar da suke takawa wajen inganta al’adun zaman lafiya da rashin tashin hankali a Nijeriya,” inji shi.
