Labarai
Tsautsayi: Direban Adaidaita Sahu ya mutu yayin wanke babu a rafi
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wani direban babur ɗin Adaidaita sahu mai shekaru ashiri da biyar Ammar Ibrahim bisa nutsewar da ya yi a cikin wani kogi.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Tattarawa da ke yankin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Haka kuma ta cikin sanarwar Saminu Abdullahi, ya ce, matashin ya gamu da tsautsayin ne a jiya Talata .
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 11:34 na safe daga wani Muhammad Sani kuma mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:55 na safe” inji sanarwar.
“Direban Adaidaita sahun yana kan hanyarsa ta komawa cikin garin Kano ne ya yi fakin a gefen titi kusa da wani kogi da nufin wanke babur ɗin nasa, amma sai tsautsayi ya ja shi cikin kogin”.
Haka kuma sanarwar ta ce, “An fito da marigayin daga cikin ruwan ne a sume amma daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa”.
Saminu Abdullahi ya ƙara da cewa an miƙa gawar marigayin ga jami’in ɗan sanda mai suna Sifeto Jerry Mathew na ofishin ƴan sanda na Dawakin Tofa.
