Connect with us

Labarai

Wasu ‘Yan Jam’iyyar NNPP, PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyya Mai Mulki

 

Kimanin ‘yayan jam’iyyu daban-daban har mutane 546 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a karamar hukumar Mallam Madori ta jihar Jigawa.

Shugaban karamar hukumar, Malam Usaini Umar BK ne ya bayyana haka a lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka a Malam-Madori ranar Laraba.

Ya’yan Jam’iyun sun hada da PDP, SDP, NNPP su Sama da 500, Sun Sauya Sheka Zuwa APC A jihar Jigawa.

Ya ce sama da magoya bayan jam’iyyun adawa 546 ne suka bar jam’iyyarsu suka koma APC gabanin zaben 2023.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Jigawa ta arewa maso gabas, Alhaji Ango Mallam-Madori ya yi maraba da wadanda suka sauya sheka daga jam’iyun nasu zuwa jam’iya mai mulki, inda ya kuma yi alkawarin daukar su kamar sauran ‘yayan jam’iyyar.

Ya bukace su da su hada kan su, su yi kokarin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Shugaban masu sauya shekar Malam Muhammad Mai Yarbawa ya ce sun bar jam’iyyarsu ne saboda rashin tsari da kuma rashin cika alkawari.

Ya kuma bada tabbacin yin aiki tukuru domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a babban zabe mai zuwa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet