Labarai
Kogi: Ƴan fashi da makami sun kai farmaki bankuna
Wasu gungun ƴan fashi da makami, sun kai farmaki bankunann Zenith da UBA da kuma First Bank duk a yankin ƙaramar hukumar Ankpa.
Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru da tsakar ranar yau Talata inda ƴan fashin suka arce da maƙudan kuɗin da ba a san adadinsu ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ƴan fashin sun je bankunan ne a cikin ƙananan motoci da babura da har ma da motoci ƙirar Bus.
Haka kuma ta ruwaito ɓata garin sun yi harbe-harben kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su tsere.
Ka zalika ta ƙara da cewa ƴan fashin sun arce ne ba tare da an yi nasarar cafke ko ɗaya daga cikinsu ba.
