Featured
Pogba zai rasa damar taka leda a gasar cin kofin duniya saboda raunin da ya samu
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Mai yiwuwa dan wasan tsakiyar Faransa da ke taka leda da Juventus Paul Pogba ba zai samu damar buga gasar cin kofin duniya ba sakamakon tiyatar da aka yi masa a gwiwa.
Paul Pogba, mai shekaru 29 da ya koma Juventus daga Manchester United ya ji rauni a gwiwarsa a watan Yuli kuma tun daga wannan lokaci bai sake murza leda ba.
Faransa za ta buga wasan farko a gasar cin kofin duniya da Australia a ranar 22 ga watan Nuwamba.
Kocin Juventus Massimiliano Allegri ya ce Pogba ya yi atisaye karo na biyu da safiyar nan amma ya dakata, kuma daga nan ne aka yanke shawarar yi masa tiyata.
A watan Nuwamba ake sa ran fara gasar ta cin kofin Duniya a Qatar a kuma kammala a watan Disamba tsakanin tawagogin kasashen 32.
