Connect with us

Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Bada Umarnin Mayarwa Alhazan Jihar Wani kudi

 

Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin Bello Matawalle, ta amince da mayar da Naira 50,000 ga kowane mutum 1,318 a jihar da suka yi aikin Hajjin bana 2022.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwamishinan yada labarai Malam Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Laraba.

Ya bayyana cewa hakan na daga cikin matakan bayar da agajin da gwamnatin jihar ke yi domin rage wahalhalun da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa hukumar alhazan ta tsara fara mayar da kudaden ne daga ranar 12 ga watan Satumba a kowace karamar hukuma 14 na jihar domin tabbatar da bin umarnin gwamna cikin gaggawa.

“Saboda haka, an shawarci alhazai da su je kananan hukumominsu inda suka biya kudinsu domin karbar Naira 50,000, daga ranar 12 ga Satumba,” ya kara da cewa.

Dosara ya kuma bayyana cewa Matawalle ya bada tabbacin kudirin gwamnati na inganta tsaro, samar da ababen more rayuwa da sauran ribar dimokuradiyya ga al’umma.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da marawa manufofinta da shirye-shiryenta goyon baya domin samun damar sauke nauyin da aka dora mata. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet