Labarai
Wasu Mahara Sun Farmaki Wasu Al’ummomi A Kauyukan Jihar Benue
Akalla mutane hudu ne rahotanni suka ce an kashe a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al’umma biyu a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Mazauna kauyen sun shaida wa jaridar Daily trust ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne tsakanin yammacin Juma’a zuwa safiyar Asabar.
“An kashe mata biyu a bayan makarantar firamare ta Yogbo da wata guda kuma a cikin al’umma a jiya Juma’a. Abin bakin ciki shine kauyen da shugaban karamar hukumar ya fito.
“A yau (Asabar) maharan sun kashe mutum daya a Ukohol. Sun kuma kona gidaje da dama a kauyuka da dama da aka kai hari a yankin,” in ji wani dan kauyen.
Wasu mazauna kauyukan kuma sun ba da labarin cewa mazauna garin sun kaurace wa wuraren da abin ya shafa saboda fargabar sake kai hari.
Shugaban Guma Mike Ubah, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin a wani sako da ya aiko.
Ubah ya ce, “An kashe mutum hudu. Uku daga cikinsu a Yogboh yayin da sauran kuma aka kashe a Ukohor a cikin wannan lokacin.”
A halin da ake ciki, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Benue, Catherine Anene, ba ta amsa kiran waya ko sakon tes da aka aika mata a wayar salula kan lamarin ba.
