Labarai
Har Yanzu Akwai ‘Yan Matan Chibok Kusan 100 A Hannun Boko Haram — Sojoji
Har yanzu akwai dalibai 98 na makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Chibok a jihar Borno daga cikin 276 da ‘yan ta’addar Boko Haram suka sace a ranar 14 ga watan Afrilu, 2014.
Shugaban sashen leken asiri na rundunar hadin guiwa ta rundunar soja ta Operation Hadinkai a arewa maso gabas, Kanal Obinna Ezuipke ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a shedikwatarsu da ke Maimalari Cantonment a Maiduguri.
Ezuipke, wanda ya bayar da labarin yadda aka ceto ‘yan matan ya ce, “A cikin ‘yan matan Chibok 276 da aka sace, ‘yan mata 57 sun kubuta a shekarar 2014, yayin da aka sako ‘yan mata 107 a shekarar 2018. An kwato ‘yan matan uku a shekarar 2019, biyu a shekarar 2021, an kuma ceto 9 a shekarar 2022. Ya kawo jimillar ‘yan mata 178 daga hannun ‘yan Boko Haram da suka tsira da kuma sauran 98.”
Da yake bayar da kididdiga kan ayyukan dakarun Operation Hadinkai a watan Agustan 2022, Kanal Ezuipke ya bayyana cewa an kashe ‘yan ta’adda 43, yayin da wasu 24 da sojojin suka kama a watan Agusta kadai, baya ga sama da mutane 100 da aka kashe a watan Satumban 2022. da kuma kwato makamai daban-daban da suka hada da bindigu AK-47 guda 129, alburusai 1,515, FN rifles 16, 3 MG, gurneti 17, da dai sauransu, a yayin gudanar da aikin.
Ezuipke ya bayyana cewa, sojoji sun samu labarin hare-hare 26 daga ‘yan ta’addan, kuma a cikin haka, an kashe sojoji biyu, wasu 9 kuma suka samu raunuka daban-daban. Ya kara da cewa sojojin sun yi sintiri 2726 da kuma kwanton bauna 982 a kan ‘yan ta’addan.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Da yake tsokaci game da kama masu kai wa Boko Haram kayan aiki, Ezuipke ya kara da bayyana cewa, daga watan Yunin 2022 zuwa yau, an kama mutane 113 wadanda ke samar da abinci, taki da sauran kayan aiki ga ‘yan ta’addan.
Ya kara da cewa sojojin sun kuma ceto mata da yara da dama, tare da lalata dukiyoyi da maboyar ‘yan ta’addan.
