Hukumar NCAA ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Azman
Hukumar kula da zirga-zirgar Jiragen sama ta Najeriya NCAA, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kamfanin Azman bisa gazawar kamfanin wajen sabunta shaidar sahale yin zirga-zirgar jiragensu.
Tun da fari dai kamfanin ne ya bayyana hakan a shafinsa na Internet yana mai shaida dakatar da tashin jiragensa a yau Alhamis.
A cewar sanarwar kamfanin ya dakatar da tashin dukkan jiragensa a faɗin Najeriya.
Sai dai har kawo yanzu babu wani sabon rahoto daga hukumar har ma da kamfanin na Azman Air.