Connect with us

Labarai

Kano: Ƴan sanda sun cafke matar da ta sheƙa wa matashi tafasasshen shayi

Rundunar ƴan sandan jahar Kano ta kama wata matashiya Maryam Haruna mai Shekaru 27 bisa zargin ta da watsa wa wani matashi Lawan Inuwa Ibrahim ɗan shekaru 25 tafasasshen ruwan Shayi a jikinsa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

ya ce “Mun samu ƙorafi ne daga wasu mutane a unguwar Rimin Auzinawa a ranar 11 ga watan Satumba, cewa wata mata mai suna Maryam Haruna ta ƙona Lawan Inuwa Ibrahim da ruwan Shayi”.

Haka kuma ya ce, “Bayan samun ƙorafin ne rundunar ta tura jami’anta ƙarƙashin Baturan yan sanda na unguwar Rijiyar Zaki CSP Usman Abdullahi inda suka garzaya da matashi asibiti tare da cafke a wadda ake zargin”.

SP Kiyawa ya ƙara da cewa, “Bayan kai shi asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad ne likitoci suka yi masa magani a fuska da hannunsa da kuma cikinsa da ya samu ƙuna tare da kwantar da shi a asibitin.

A nata ɓangaren, Wadda aka cafke ɗin ta amsa cewa ta watsa masa ruwan kuma ta yi hakan ne sakamakon rikici da ya ɓarke a tsakaninsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet