Labarai
Jigawa: Wadanda Suka Rasa Ransu Sun Doshi 100 A Sanadin Ambaliya
Hukumomi a jihar Jigawa sun bada rahoton mutuwar mutane shida sakamakon ambaliyar ruwa da ke ci gaba da yin barna a cikin al’ummar jihar da ke Arewa maso yamma.
Hakan na zuwa ne kwanaki uku da hukumomin ‘yan sanda a Jigawa suka ce wasu mutane 29 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar ambaliyar ruwa. Ya zuwa ranar Talatar nan, jihar ta yi asarar mazauna 98 sakamakon mummunar ambaliyar ruwan.
Shugaban hukumar da da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), Sani Babura, wanda ya tabbatar da mutuwar mutane shidan, ya koka da yadda ambaliyar ruwa a jihar ta kai wani mataki mai ban tsoro.
Ya bayyana cewa a kowace rana adadin al’ummar da ambaliyar ta shafa na karuwa, lamarin da ya ce ya kara ta’azzara.
Sani ya alakanta mutuwar da ambaliyar ruwan sama da kuma walkiya, inda ya kara da cewa kawo yanzu akalla mutane 57,000 ne suka mutu.
A cewarsa, sama da mutane 100,000 ne aka tilastawa barin gidajensu, kuma wasunsu na zaune ne a sansanoni 49 da gwamnatin jihar ta kafa domin samar wa ‘yan gudun hijira mafaka.
“Game da filayen noma, tituna, da sauran ababen more rayuwa da ambaliyar ta lalata, ana ci gaba da tantancewa kuma za a fitar da kididdigar, amma barnar na da yawa,” in ji shugaban SEMA.
Sai dai ya bayar da tabbacin hukumar tana aiki na sa’o’i 24 tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa (NEMA) da sauran abokan hulda domin tallafawa wadanda abin ya shafa.
Akalla mutane 83 da suka hada da yara da mata ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar tun daga farkon watan Agusta.
Ambaliyar ta kuma yi illa ga ababen more rayuwa a jihar, yayin da wasu tituna suka katse sakamakon zaizayar kasa, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin neman wasu hanyoyin da za su bi.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, A kwanakin baya ne hukumar kula da ruwa ta Kasa NIHSA ta tabbatar da jihar Jigawa a matsayin jihar da ta fi fama da matsalar ambaliyar ruwa da ta addabi sassan kasar nan.
Ta ce kananan hukumomi 16 na jihar ne lamarin ya shafa sannan sama da mutane 72 ne suka mutu tare da lalata dukiyoyi, abubuwan more rayuwa, da na amfani a ranar 7 ga watan Satumba.
