Connect with us

Labarai

Wata Ambaliyar Ruwa Ta Shafi Al’ummomi 13, Wasu Sun Bar Muhallansu

Al’ummomi 13 a karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar iyalai 300 sun rasa gidajensu.

Makarantu, coci-coci, kasuwanni, filayen noma da gidajen zama a cikin al’ummomin ruwa ya mamaye su, yayin da wasu mazauna garin suka koma garuruwan makwabta.

Al’ummomin da abun ya fi shafa su ne Ogwuikpele da Akali Ogidi da ke gefen kogin Neja.

Sauran al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Atani, Osamala da Umu-Uzu wadanda suma ke kan gabar tekun Nijar.

Shugaban al’ummar Ogwuikpele, Mista Madupuo Sunday Victor, wanda ya zanta da jaridar Daily trust, ya ce akwai bukatar a samar da mafita ta din-din-din don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke faruwa.

“Muna zaune kusa da kogin Neja kuma ya mamaye bakunansa, kuma wannan mafari ne. Ba mu da sansanonin ‘yan gudun hijirar da waɗannan mutanen za su iya zama.

“Muna buƙatar kulawar likitoci kuma muna buƙatar kayan agaji saboda yara da mata masu shayarwa yanzu sun kasance masu saurin kamuwa da kowane irin cututtuka,” in ji shi.

Shugaban al’ummar Akiri Ogidi, Michael Chukwuse, ya ce ambaliyar ta jawo iyalai da dama cikin wahala.

“Muna kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi da su kawo mana agaji a halin yanzu domin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) kuma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Anambra (SEMA) ba za ta iya sauke nauyin da ke kanta ba.

“Abin da muke fuskanta a cikin al’ummominmu shine wanda rashin agaji ya jefa mutanenmu cikin yunwa babu taimako a gare mu” in ji shi.

Da aka tuntubi babban sakataren hukumar ta SEMA, Mista Paul Odinigbo, wanda ya tabbatar da ambaliyar ta wayar tarho, ya ce hukumar ta shiga yankin ne domin kwashe mutanen zuwa tudu.

Sai dai ya ce tun da farko hukumar ta gargadi mutane game da ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta Kasa (NiMet) ta yi hasashe har ma ta ziyarce su kan shirin wayar da kan jama’a.

“Ambaliya ba bisa katsam ba ce, sun san za a yi ambaliya. Mun gargade su har ma mun kai ziyarar wayar da kan jama’a ga dukkan al’ummomin da akayi tsammani.

“Mun bukaci su kwashe kafin ambaliyar ta zo. Ba wai a Ogbaru kadai muke da ambaliyar ruwa a jihar ba. Muna da wasu al’ummomi kusan bakwai a jihar da ambaliyar ta shafa,” inji shi.

Shima da aka tuntubi Kwamishinan Muhalli na Jihar Anambra, Felix Odumegwu, ya ce gwamnatin jihar ta fara duba al’ummar da lamarin ya shafa, inda ya ce za a samar da sansanonin ‘yan gudun hijira na cikin gida ga wadanda abin ya shafa.

Ya kuma ce an baza kungiyoyin likitoci a yankunan da lamarin ya shafa domin taimakawa wadanda abin ya shafa.

Odumegwu ya kara da cewa, “Ambaliya dabi’a ce kuma bala’i ne amma mun fara tun da wuri don gudanar da gangamin wayar da kan jama’a kafin ambaliyar, kuma a halin yanzu muna yin cudanya da Hukumar NEMA da namu na SEMA don taimaka wa wadanda ambaliyar ta shafa,” Odumegwu ya kara da cewa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet