Connect with us

Labarai

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Gargadi Yan Siyasa, Yayin Da Ake Shirin Fara Kamfen

 

Rundunar ‘yan sanda ta gargadi shugabannin siyasa a jihar Kano da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Abubakar Lawal ne ya yi wannan kiran yayin taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyun siyasa lokacin da ake shirin fara yakin neman zabe.

Ya ce taron an yi shi ne domin wayar da kan daukacin shugabannin jam’iyyar siyasa a jihar kan bukatar a zauna lafiya a duk lokacin yakin neman zabe.

Kwamishinan ya gargadi ‘yan siyasa game da kalaman nuna kiyayya, tsokana kalamai a kafafen yada labarai, wuce gona da iri na ‘yan jarida, amfani da muggan kwayoyi da ‘yan daba, da kuma harba makamai a lokacin ayyukan jam’iyyun siyasa.

Ya bukaci shugabannin jam’iyyar siyasa da su yi nasara kan magoya bayansu su kasance masu kyakykyawan hali ta hanyar gujewa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar da ake samu a jihar.

“Ba za mu amince da duk wani yunkuri da wata jam’iyyar siyasa za ta yi na haifar da rikici a Jihar ba domin duk wanda aka kama zai fuskanci fushin doka,” inji shi.

Shugabannin jam’iyyun siyasar sun yi alkawarin zama masu bin doka da oda a dukkan harkokinsu na siyasa

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet