Labarai
Da-Ɗumi-ɗumi: Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Burkina Faso
Rahotonni da ke fitowa daga ƙasar Burkina Faso a yanzun nan na tabbatar da cewa Kyaftin Ibrahim Taro are, ya kifar da gwamnatin mulkin soji ta Paul Henri Damiba.
Paul Henri Damiba, dai shi ne sojan da ya yi juyin mulki ga gwamnatin ƙasar ta farar hula ta shugaba Kabore, tun a ranar 24 ga watan Janairun bana.
