Connect with us

Labarai

Hukumar PSC ta yi wa manyan ƴan sanda 417 ƙarin girma

Hukumar kula da ayyukan ƴan sanda ta ƙasa PSC, ta yi ƙarin girma ga manyan jami’an ƴan sanda su ɗari huɗu da goma sha bakwai.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ta PSC Ikechukwu Ani ya fitar da yammacin Juma’ar nan.

Haka kuma sanarwar ta ce “Hukumar PSC, ta kuma amince da ƙarin girma ga kwamishinonin ƴan sanda guda goma sha biyu zuwa matsayi na gaba na mataimakin babban sufeto watau AIG.”

Haka kuma hukumar ta amince da jarabawar karin girma ga jami’an ƴan sanda da aka shirya za a fara daga farkon shekarar bara.

Hukumar ta PSC, ta bayyana hakan ne yayin babban taron ta karo na goma sha biyar da aka gudanar a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin muƙaddashin shugaban hukumar Justice Clara Bata Ogunbiyi mai Ritaya.

Hukumar ta kuma amince da naɗin AIG Bello A. Sadiq, wanda a yanzu shi ne mataimakin babban sufeto mai kula da shiyya ta daya ta rundunar da ke nan Kano, da kuma AIG Dandaura Mustapha, mai kula da shiyya ta huɗu da ke Makurdi, zuwa mukamin mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet