Labarai
Kaduna: Hukumar NDLEA ta cafke mutane 121 bisa zargin safarar ƙwayoyi
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA shiyyar jihar Kaduna, ta ce, ta cafke mutane ɗari da ashirin da ɗaya bisa zarginsu da safarar miyagun kwayoyi tare da rufe gidajensu goma sha uku.
Kwamandan hukumar ta NDLEA shiyyar jihar Umar Adoro, ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau Litinin.
Ya ce, hukumar ta kuma lalata miyagun ƙwayoyi har kala ashirin da bakwai.
Kwamandan na hukumar NDLEA shiyyar Kaduna, ya ƙara da cewa gidajen da aka kama miyagun ƙwayoyin ta gano su ne a unguwannin Kawo da Kabala da Numba Zango da Sabon gari da titin Nupe da Unguwar Mu’azu da kuna birnin Zaria.
Sai Unguwar shanu da Maraban Jos da Dan Magaji da Hayin Banki da Kafanchan da sauransu.
Umar Adoro, Ya ƙara da cewa a cikin mutanen ɗari da ashirin da ɗaya da hukumar ta cafke goma sha uku mata ne.
Kwamandan ya ce, miyagun ƙwayoyin da hukumar ta kama ɗin sun haɗa da tabar wiwi mai nauyin Kilogirman 247,172 da hodar Ibilis mai nauyin kilo giram 0.041sai ƙwayar heroine mai nauyin Kilogiram 0.363 da Tramadol Kilogiram 74,441da sauransu.
