Featured
Bai kamata a rika ruda Messi da kiraye-kirayen komawa Barcelona ba- Xavi
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Xavi Hernandez ya yi kira da kada a raba wa Lionel Messi hankali bayan jita-jitar da ke ci gaba da yawaita kan yiwuwar dan wasan gaban na Parsi Saint-Germain ya koma Camp Nou da taka leda bayan karewar kwantiraginsa.
A karshen wannan kaka ne, kwantiragin Messi mai shekaru 35, zai kare a PSG yayinda a makon da ya gabata, mataimakin shugaban Barcelona, Eduard Romeu ya bayyana cewa zai yi matukar armashi idan tsohon kaftin din nasu ya dawo Camp Nou da taka leda.
Kalaman Romeu na zuwa ne bayan da shugaban kungiyar, Joan Laporta ya nuna kamar kofa a bude ta ke ga Messi idan ya na son dawowa a wata ganawa da ya yi da wata jaridar wasanni.
Batun komawar Messi Barcelona ya zo ne biyo bayan samun darewar kungiyar saman teburin La Ligar Spain a asabar da ta wuce, karon farko kenan cikin sama da shekaru 2.
Sai dai a yayinda har yanzu ba a doke su a La Liga ba, suna da aiki ja don kaucewa gaza tabuka wani abu a matakin rukuni na gasar zakarun Turai.
