Connect with us

Ilimi

Kungiyar Malamai Ta Bukaci Gwamnonin Jihohi Da su Biya Bashin Albashin Ariyas

 

 

Kungiyar malamai ta Kasa NUT a ranar Talata ta yi kira ga gwamnonin da ake bin bashin albashin ariyas din malaman da su yi amfani da ragowar watannin da suka rage a kan karagar mulki wajen biyan basussukan da suke bi.

Babban sakataren kungiyar, Dr Mike Ike-Ene ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Abuja, gabanin bikin ranar malamai ta duniya.

DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Ranar malamai ta duniya mai taken: “Malamai a zuciyar farfaɗowar ilimi’ a ranar 5 ga watan Oktoba, kowace shekara, don nuna godiya ga malamai saboda manyan ayyukansu.

Ike-Ene ya ce gwamnonin jihohi da dama malaman firamare da na sakandare na bin su bashin albashin watanni.

“Da yawa daga cikin wadannan malaman sun koka kan gazawa da rashin bin ka’ida da jihar ke fama da su wajen biyan albashin ma’aikata da kuma lokacin da ya kamata biyo bayan halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki.

“Wasu gwamnatocin jihohi, malaman firamare na bin su bashin albashi daga watanni hudu zuwa 18,” inji shi.

Sai dai ya yabawa gwamnonin jihohin da suka jajirce wajen biyan albashin malamai a lokacin da ya kamata.

Babban sakataren ya kuma ja hankalin malamai da su ci gaba da aiki tukuru ba tare da la’akari da ma’aunin albashin su ba.

Ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su samar da yanayin da malamai zasu iya aiki yadda ya kamata.

“Lokacin da malami ya shiga cikin aji, akwai wasu abubuwa da malamin yake nema kuma idan waɗannan abubuwan suna nan yana iya yin aiki da kyau,” in ji shi.

Ike-Ene ya ce sabbin shekarun ritayar malaman daga shekara 60 zuwa 65 da kuma shekaru 35 zuwa 40 na hidima sun kai kashi 90 cikin 100 na aikin.

“An sanya hannu kan daya daga cikin manyan alkawuran; batun shekaru 65 da 40, an sanya hannu kan karuwar shekarun hidimar malamai ko shekarun ritaya. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet