Labarai
Dan Arewa Maso Gabas Ne Zai Gaji Ayu Shugaban Jam’iyya Na KasaIdan Ya Yi Murabus – Tsohon Sakataren PDP
Tsohon sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Emmanuel Agbo, ya ce idan shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga yankin Arewa maso Gabas zai maye gurbinsa.
Da yake jawabi a kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a gidan talabijin na Arise, Dr Agbo, ya ce ko da Ayu ya yi murabus da gangan, wanda zai karbi mukamin shi ma ya fito daga yankin Arewa maso Gabas kamar yadda ya bayyana a kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
An samu rikici a jam’iyyar PDP tun bayan zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu ya doke gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da sauran su.
Wike ya caccaki fitowar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa, da Ayu, shugaban jam’iyyar.
Wike ya zargi jam’iyyar da keta ka’idojin daidaito, adalci da gaskiya, inda ya bukaci Ayu ya yi murabus domin dan kudu ya zama shugaban jam’iyyar.
Ya ce, “35 karamin sashe na 3 na kundin tsarin mulkin PDP ya ce idan wani jami’i ya yi murabus da gangan, ko kasawa ko kuma ya mutu, yanzu a ce shugaban jam’iyyar na kasa kamar yadda lamarin yake, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a shiyyar da ya zo ne zai karbi ragama.
“Idan Ayu ya yi murabus a yau, wanda zai karbi mukamin Umar ne daga Arewa maso Gabas. Kuma Umar ba dan Arewa kadai yake ba, amma daga Arewa maso Gabas ne inda dan takararmu na shugaban kasa ya fito.
“Suna kira da ya yi murabus (Ayu)… Akwai cikas ga tsarin mulki ga wannan kiran”.
