Labarai
Hukumar NEMA Ta Raba Kayayyakin Tallafi ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta raba kayan agaji ga mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kananan hukumomi tara na jihar Kogi.
Mista Justin Uwazuruonye, shugaban aiyuka na NEMA na Abuja ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
A cewarsa, kayayyakin abincin da aka raba sun hada da shinkafa, wake, masara, gishiri, mai, tumatur, tabarma, gidan sauro, sabulu da tufafi.
“Wannan gaggawar da Gwamnatin Tarayya ta yi ta hannun Hukumar NEMA, karkashin jagorancin Mista Mustapha Ahmed, ita ce ta dakile illar ambaliyar ruwa da ta raba dubban mutane da muhallansu a bana.
“Ya zuwa yanzu, mun raba wadannan kayayyakin ga wadanda abin ya shafa a kananan hukumomi tara na jihar, wato; Lokoja, Kogi, Igalamela da Odolu, Ajaokuta, Ofu, Omala, Bassa, Ibaji da Idah,” inji shi.
Uwazuruonye ya ce an yi rabon kayayyakin ne tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kogi (KGSEMA) a makarantar firamare ta St. Luke’s, Adankolo.
Wadanda ambaliyar ruwan ta shafa na zama na dan wani lokaci a makarantar.
Kamfanin dillacin labarai na Kasa NAN ya rawaito cewa, Mista Edward Onoja, mataimakin gwamnan Kogi, wanda ya halarci wajen rabon ya godewa gwamnatin tarayya, ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i da kuma hukumar NEMA bisa daukar matakin da ya dace.(NAN)
