Connect with us

Featured

El Clasico: Courtois ya kammala murmurewa

Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa

 

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti yana sa ran mai tsaron gidan kungiyar Thibaut Courtois zai dawo daga jinyar raunin da ya tafi, inda ake sa ran zai kasance a wasan El Clasico da Barcelona ranar Lahadi.

Courtois bai buga wa Madrid wasa ba tun bayan da suka doke Atletico Madrid da ci 2-1 a ranar 18 ga Satumba.

Mai tsaron ragar bai samu damar buga wasanni uku ba a dukkanin wasannin La liga da na zakarun Turai sannan kuma ba zai buga wasan da Madrid za ta je Warsaw don karawa da Shakhtar Donetsk a gasar zakarun Turai na Yau Talata.

Amma abu mai mahimmanci, mai tsaron ragar wanda Ancelotti ke da kwarin gwiwa a kan sa, ana hasashen zai kasance a fafatawar da Madrid za ta yi da Barcelona a ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Yayin da Courtois ba zai buga wasa a Poland ba, Karim Benzema na shirin kasancewar cikin tawagar da zata wakilci Real Madrid din.

Benzema ya yi jinyar makwanni uku bayan ya samu rauni a cinyarsa a gasar cin kofin zakarun Turai da suka doke Celtic a watan jiya kafin ya dawo wasan da suka tashi 1-1 da Osasuna a ranar 2 ga Oktoba.

Amma Vinicius Junior, wanda ya buga dukkan wasanni 12 da Madrid ta yi a kakar wasa ta bana, na iya samun hutu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahisjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet