Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Zamfara Ta Bude Makarantu 45 Cikin 75 Da Ta Kulle Saboda Tsaro

Gwamnatin jihar Zamfara ta bude makarantu 45 daga cikin 75 da ta rufe saboda rashin tsaro, kamar yadda ma’aikatar ilimi ta sanar a ranar Larabar nan a Gusau.

Babban Sakatare a ma’aikatar, Alhaji Kabiru Attahiru ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar ilimin fasaha ta jihar a cikin gaggawa (EiE) wadanda suka kai ziyarar neman shawara a ma’aikatar.

Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe makarantun ne a watan Satumbar 2021 bayan sace daliban makarantar Sakandare ta gwamnati da ke garin Kaya a karamar hukumar Maradun ta jihar.

“Yayin da muka sake bude makarantun, mun kasasu kashi uku – Green, Yellow and Red.

“Green sun kasance makarantu a wuraren da babu barazanar tsaro, Yellow na makarantun da ke yankunan da ke da ƙananan barazanar rashin tsaro, yayin da Red suka kasance makarantu a yankunan da ke da hadarin tsaro,” in ji Attahiru.

Ya ce dukkan makarantun 75 sun fada cikin yankin Red group a lokacin da aka rufe su saboda da akwai hadari a bar su a bude.

“A yau, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, sakamakon inganta tsaro a jihar, mun bude makarantu 45 daga cikin 75, yayin da 30 daga cikin makarantun suka kasance a rufe.

“Gwamnati da jami’an tsaro sun yi aiki tare domin tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar.

“Muna fatan a kara inganta harkokin tsaro a jihar domin mu sake bude sauran makarantu 30,” inji shi.

Babban Sakataren ya yaba wa tawagar EiE bisa wannan ziyara tare da ba su tabbacin ma’aikatar ta kudiri aniyar ci gaba da hada hannu da duk masu ruwa da tsaki domin bunkasa harkar ilimi a jihar.

“Wannan abin farin ciki ne. Ina ɗaukar wannan ƙungiyar a matsayin abokan tarayya na ci gaba. Ina ba ku tabbacin cikakken goyon baya da haɗin gwiwar ma’aikatar, ”in ji shi.

Tun da farko, shugabar tawagar, Hajiya Sa’adatu Abdu-Gusau, ta bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin bayar da shawarwarin kafa kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Education in Emergency Working Group (EiEWG) a jihar.

Abdu-Gusau, wanda shi ne Daraktan Tsare-tsare da kididdiga a ma’aikatar, ya ce ziyarar bayar da shawarwarin kuma na daga cikin ayyukan tunawa da ranar yara mata ta duniya. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet