Ilimi
Ƙungiyar ASUU ta dakatar da yajin aikin da take yi
Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta janye yajin aikin da ta kwashe tsawon watanni takwas tana yi.
Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, wakilin jaridar ya tattaro cewa an dauki matakin ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa ta kungiyar da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.
Dakta Chris Piwuna, mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar wa BBC labarin, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar yau Juma’a, bayan da shugabannin kungiyar suka gana cikin dare a Abuja babban birnin tarayya.
Kotun kolin Najeriya ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin gabanin ta saurari daukaka karar da ta yi a gabanta.
