Labarai
Dan Arewa Baya Bukatar Dan Takarar Yarabawa Ko Ibo, Dan Arewa Yake Bukata – Atiku
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya jaddada cewa shi ne ya fi cancantar shugabancin kasar nan, inda ya ce ‘yan Arewa na bukatar wani daga yankin a matsayin shugaban Najeriya a 2023.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne ya yi wannan tsokaci a wani taron tattaunawa na siyasa na Arewa Town Hall a Kaduna.
“Na ratsa duk fadin kasar nan,” in ji Atiku, wanda ya fito daga Adamawa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, a ranar Asabar.
“Na san duk kasar nan. Na gina gadoji a fadin kasar nan. Ina ganin abin da talakan Arewa ke bukata shi ne wanda ya fito daga Arewa, wanda kuma ya fahimci sauran sassan Najeriya, kuma ya iya gina gadoji a fadin kasar.
“Wannan shi ne abin da dan Arewa yake bukata. Shi (dan arewa) baya bukatar dan takarar Yarbawa ko dan kabilar Ibo. Wannan shi ne abin da dan arewa yake bukata. Na tsaya a gabanku a matsayina na dan Najeriya dan asalin arewa.”
Bidiyon kalaman Atiku da ya fito bayan sa’o’i a shafukan sada zumunta, ya janyo cece-ku-ce daga ‘yan Najeriya da jam’iyyun siyasa ciki har da jam’iyyar APC mai mulki.
Kakakin jam’iyyar APC Felix Morka ya bayyana kalaman da dan takarar PDP ya yi a matsayin mai raba kan jama’a, yana mai cewa kasar nan ba ta bukatar hakan.
