Connect with us

Labarai

Shugaban Kasa Buhari Ya Koka Kan Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Shafi Wasu Jihohi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda ambaliyar ruwa ta afku a Bayelsa da sauran jihohin Najeriya.

Sannan shugaban ya koka da yadda ambaliyar ta yi barna a Jihohi 33 a fadin kasar nan.

Kazalika Buhari ya umurci dukkanin hukumomin tarayya da ke kula da ayyukan ceto da magance bala’o’i da su ba da tallafin da ake bukata ga jihohin.

Rahotannin da gwamnatin jihar Bayelsa ta fitar sun ce kimanin mutane 700,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin al’ummomi da kauyuka kusan 300 a kananan hukumomi biyar daga cikin takwas na jihar.

Sai dai Buhari ya dora laifin ambaliya kan rashin kula da alamun gargadi da kuma toshe hanyoyin ruwa da mazauna yankin ke yi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu ya fitar, ta ce, “Buhari ya zargi yin gine-gine a kan magudanan ruwa, rashin kula da gargadin farko da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA ta yi, da kuma sauyin yanayi da ke haifarwa a matsayin babban laifin ambaliya.”

“Ya zuwa yanzu dai ya shafi jihohi 33 daga cikin 36 na kasar, da kuma babban birnin tarayya wanda shi ma bai tsira ba.”

Ya ba da umarnin cewa duk inda abin ya faru “da su yi aiki don maido da al’ada a duk sassan tarayyar da abin ya shafa.”

Shugaban ya jajantawa iyalan wadanda iftila’in ya shafa da kuma duk wadanda ambaliyar ta shafa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet