Featured
Bacin rai ne ke tunzura ni wajen aikata abin da banyi nufi ba- Ronaldo
Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa yanayin bacin ran da ya ke fuskanta ne ya kai shi ga aikata abin da ya sa aka cire shi daga wasan da kungiyar ta kara da Chelsea a ranar asabar da ta gabata.
Kalaman na Ronaldo na zuwa bayan yawaitar korafe-korafe kan dabi’un da ya ke nunawa a baya-bayan nan, musamman bayan ficewarsa daga fili a wasan da United ta yi nasara kan Tottenham da kwallaye 2 da nema, lokacin da ya tabbatar da cewa mai horarwa Erik ten Hag bashi da shirin amfani da shi duk da kasancewarsa cikin ‘yan wasan da ke zaune a benci don yin sauyi da su.
Cikin wani sako da dan wasan gaban na Portugal mai shekaru 37 ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce ya na iyakar kokarinsa wajen zama kyakkyawan misali kan ‘yan wasa masu tasowa amma a lokuta da dama yanayin tunzurawa da kuma bacin rai ke kaishi ga yin abubuwan da bai nufaci aikatawa ba.
A cewar Ronaldo wani lokacin irin wannan yanayin alfanu ne gareshi, domin kuwa shi kansa ba zabinsa bane kasance a irin wannan yanayi mai cike da matsin lamba, sai dai ya gamsar da kansa cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa tare da taimakon abokanan wasansa a filin wasa da kuma shiga duk karawar da aka ga ya dace ayi da shi.
