Connect with us

Featured

Lewandowski ya ci kwallo ta 601 bayan nasarar Barcelona kan Villareal

Daga Abdu Ado Ƙofar Na’isa

Robert Lewandowski ya yi nasarar cin kwallo ta 600 da kuma 601 a tsawon lokacin da ya shafe yana kwallo tsakanin manyan kungiyoyin Turai, yayin wasan da Barcelona ta yi nasara kan Villareal da kwallaye 3 da nema.

Wasan na jiya Juma’a wanda ya zo bayan shan kayen Barca da kwallaye 3 da 1 a hannun Real Madrid lahadin da ta gabata, kungiyar ta samu dukkanin kwallayenta 3 cikin mintuna 7 kadai tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan kwallayen na Lewandowski 2 Ansu Fati ne ya cike kwallon ta 3 wanda ya baiwa kungiyar ta Catalonia damar rage tazarar da ke tsakaninta da Madrid jagora zuwa maki 3 a teburin La Liga.

Nasarar ta jiya dai ita ce karon farko cikin wasanni 3 da Barcelona ta doka a baya-bayan nan, kuma ita ce kwallo ta 16 da Lewandowski ya zurawa kungiyar tasa cikin wasanni 14 da ya doka tun bayan zuwansa daga Bayern Munich.

Haka zalika Lewandowski mai shekaru 34 ya zama dan wasan na farko bayan Ronaldo da Messi wanda yawan kwallayensa ya haura 600 tun daga shekarar 2000 zuwa yanzu.

A tsawon lokacin da ya shafe a Bayern Munich Lewandowski ya zura kwallaye 344 a wasanni 375 yayinda ya zura kwallaye 103 a wasanni 186 yayin taka ledarsa a Brossia Dortmund.

Dan wasan ya kuma zura kwallaye 21 yayin taka ledarsa a Znicz Pruszkow sai wasu kwallaye yayin zamansa a kungiyar Lech Poznan ta Poland baya ga wasu kwallaye 76 da ya zurawa kasarsa Poland a wasanni 134 da ya doka mata.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet