Connect with us

Labarai

Duk Da Barazanar Tsaro Atiku Isa Edo Don Yakin Neman Zaben

Duk da ana cikin tabarbarewar tsaro, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya isa jihar Edo domin yakin neman zabensa na shugaban kasa gabanin babban zabe na 2023.

Atiku ya isa filin jirgin sama na birnin Benin tare da mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da mataimakinsa Philip Shuaibu da kuma manyan ‘yan siyasa da jami’an jam’iyyar PDP da mambobin jam’iyyar PDP ne suka tarbe shi a filin jirgin.

Da isarsa, magoya bayansa da suka hada da kungiyoyin mata da matasa suka yi ta buga ganguna domin tarbarsa yayin da suke rera sunansa domin nuna goyon baya.

Daga filin jirgin, Atiku da tawagarsa sun ziyarci fadar Sarkin Benin, mai martaba Oba Ewuare II (na biyu) inda suka nemi alfarmar sarkin bisa burinsu.

Ya ce sarkin na da rawar da zai taka wajen samar da shugabanci ga kasa.

Da yake mayar da martani, Sarkin ya tabbatar wa Atiku da addu’o’in fadarsa.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Atiku ya ziyarci Edo duk da barazanar tsaro a jihar. A ranar Juma’ar nan ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa ayarin motocin babban mai kula da ma’aikatar kashe gobara ta Omega, Apostle Johnson Suleiman hari inda suka kashe mutane shida ciki har da jami’an tsaron da ke tare da shi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin jihar Edo ta ce ta bankado shirin da wasu mutane ke yi na kawo cikas a yakin neman zaben shugaban kasa.

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Osarodion Ogie ya fitar ta ce gwamnati za ta tabbatar da gurfanar da masu kokarin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar kamar yadda doka ta tanada.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet