Labarai
Hukumar DSS Ta Bukaci Al’umma Da Su Kwantar Da Hankulansu
Hukumar tsaro ta DSS a daren Lahadi ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da lura da sanarwar bayar da shawarwarin tsaro da ofishin jakadancin Amurka ya yi wa ‘yan kasar kan yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a kasar, musamman a babban birnin tarayyar kasar Abuja.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta, Dr Peter Afunanya ya raba wa manema labarai a Abuja.
Sanarwar ta ce: “Hukumar tsaron DSS ta samu tambayoyi da dama dangane da shawarwarin tsaro da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya bayar, a yau 23 ga watan Oktoba 22.”
“Idan Jama’a za su iya tuna cewa Ma’aikatar ta yi irin wannan gargadi daban-daban a baya”.
“Yayin da yake ba da shawarar cewa kowa da kowa ya ɗauki matakan da suka dace, an umarci jama’a da su kasance cikin faɗakarwa tare da taimakawa jami’an tsaro da bayanai masu amfani game da barazanar da kuma aikata laifukan da ke kewaye da su.”
“A halin da ake ciki, rundunar ta yi kira da a kwantar da hankula yayin da take aiki tare da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Abuja da wajen Abuja.”
