Labarai
Jarabawar NECO, WAEC, NBAIS Duk Zasu Kasance Kyauta Idan Aka Zabe Ni – Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jarrabawar kammala karatun sakandare a Najeriya ta NECO, WAEC, NABTEBE, NBAIS, duk zasu kasance kyauta ne ga dalibai yan kasar.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yau, yayin da yake bayyana kundin manufofin takararsa ta shugaban ƙasa (Blueprint) idan har yayi nasarar zama shugaban ƙasa a zaben 2023.
Kwankwaso yana taron ƙaddamar da jadawalin kundin manufofin takararsa a babban birnin tarayyar Abuja, inda yace za’a kara wa’adin jarabawar neman gurbin shiga jami’a ta JAMB zuwa shekaru hudu kafin ta daina aiki.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Kwankwaso dan takara ne da yayi fice wajen baiwa bangaren ilimi fifiko, tare da taimakon dalibai.
