Connect with us

Labarai

Majalisar ‘Yan Jaridu Ta Dakatar Da Ayyukanta Da Gwamnatin Jihar Yobe

 

Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Yobe, NUJ, ta dakatar da ci gaba da aiki tare da gwamnatin a jihar

Matakin dakatarwar da kuma kauracewa tarukan gwamnan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Ahmed Abba da sakatarenta Michael Oshomah suka sanyawa hannu tare da rabawa manema labarai a ranar Talatar nan a Damaturu.

“Bayan sanarwar kauracewa taron da aka baiwa gwamnatin jihar Yobe a baya dangane da ayyukanmu a jihar, shugabannin kungiyar masu aiko da rahotanni sun gana da shugaban ma’aikata na gwamna Mai Mala Buni, Abdullahi Yusuf Gashu’a, inda aka yanke hukuncin hakan, da nufin warware matsalolin,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa, a zamanta na majalisar ta Chapel ta amince da dakatar da kaurace wa ayyukan gwamnati, saboda alkawarin da jami’an gwamnatin jihar suka dauka.

“Kungiyar tana son sanar da jama’a cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata”.

A kwanakin baya ne kungiyar ‘yan jarida ta fitar da sanarwa, inda ta kauracewa duk wasu ayyukan gwamnatin jihar Yobe bisa zargin cin zarafin da jami’an tsaro da ke gidan gwamnati ke yi wa mambobinta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet